Ƙasar Amurka ta dakatar da bayar da duk wani taimako ga ƙasashen duniya, a cikin wata sanarwa da aka fitar a jiya Juma’a.

 

Sai dai ƙasar ta Amurka ta ce banda taimakon da ta ke bayarwa a ɓangaren abinci, da kuma tallafin kuɗi ga sojojin Isra’ila da ƙasar Masar.

Sakataren Amurka ne ya aike da wata takardar hakan bayan da sabon shugaba Trump ya shiga ofishinsa, da ƙudurin fifita Amurka da dakatar da taimakon ƙasashen duniya.

Umarnin ya shafi dakatar da duk wani sabo ko kuma taimako da ake bayarwa, haka kuma ya shafi taimakawa sojojin da su ke yaƙi a Yukren, da kuma taimakon magance cuta mai karya garkuwar jiki da sauransu.

Ƴan majalissu daga jam’iyyar adawa ta Democratic sun bayyana cewa, sama da mutane miliyan 83 ne su ka dogara da tallafin bayar da magunguna cututtuka daban-daban a ƙarƙashin ƙasar ta Amurka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: