Kungiyar Gwamnonin jam’iyyar PDP sun tabbatar da cewa jam’iyyarsu ta PDP ce za ta samu nasara akan Jam’iyyar APC a yayin zaben shugaban Kasa na shekarar 2027 da ke tafe.

A wata sanarwa da hadimin gwamnan Jihar Bauchi Lawal Mu’azu ya fitar, ya ce gwamnonin sun bayyana cewa su na da tabbatacin cewa PDP ce za ta mulki Najeriya 2027.

Gwamnonin sun bayyana hakan ne a yayin taron kungiyar gwamnonin jam’iyyar ta PDP, wanda aka gudanar a Jihar Delta a jiya Juma’a.

Gwamnonin sun kara da cewa su na da yakinin cewa ‘yan Najeriya za su zabi PDP a yayin zaben Kasar, don kara farfado da arzikin Kasar da ya lalace.

Kazalika sun kuma sake jaddada aniyar cewa ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da nasarar jam’iyyar a zaben mai zuwa.

Bugu da kari sun kuma yi kira ga ‘yan Kasar da su ci gaba da hakuri da dukkan halin matsin da ake fuskanta a kasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: