Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Sarkin Masarautar Udo-Eguare Friday Onojie da ke karamar hukumar Igueben ta jihar Edo.

‘yan bindigar sun yi garkuwa da Sarkin ne a gurin wani daji da ke tsakanin Kauyen Ubiaja da ke kusa da Rest House Junction da ke kauyen na Udo.

Wasu Rahotanni sun bayyana cewa ƴan bindigar sun bude wuta, inda suka hallaka wani mai babur a lokacin tsere da Sarkin.

Wata majiya a yankin ta ce ‘yan bindigar sun kuma hada da wasu mutane biyar a yayin garkuwa da Sarkin.
Amma Majiyar ta ce guda daga cikin mutane biyar din da maharan suka yi garkuwa da su tare da sarkin ya kubuta daga hannunsu tare da dawo gida.

Kakkin rundunar ‘yan sandan Jihar Moses Yamu, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

Acewarsa rundunar ta samu rahoton garkuwa da Sarkin da mutane ne a gurin wani matashi mai shekaru 21.

Kakakin ya kara da ce Basaraken na Kan babur ne a matsayin fasinja akan wata hanya wadda ba a cika binta ba zuwa garin, inda ‘yan bindiga suka yi masu kwanton bauna suka harbe matukin babur din sannan suka tsre da sarkin.

Yamu ya ce kwamishinar ‘yan sanda ta jihar Betty Otimenyin ta bayar da umarnin aikewa da jami’an tsaro na musamman zuwa yankin da lamarin ya faru, don ganin sun kubtar da basaraken da sauran mutanen.

Leave a Reply

%d bloggers like this: