Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya bayyana cewa babu wani sabani da ke tsakaninsa da tsohon gwamnan Jihar da ya gada Malam Nasir El’Rufa’i.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a jiya Litinin a wata fira da aka yi dashi a gidan Talabijin na TVC.
Uba Sani ya bayyana cewa alakar da ke tsakaninsa da El’Rufa’i tananan kamar yadda ta ke, ku babu wata matsala a cikinta.

Gwamna Sani ya bukaci mutane da su yi watsi da jita-jitar cewa ba sa ga Muciji da tsohon gwamnan Jihar Nasir El’Rufa’i, inda ya ce alakarsu nanan daram kamar yadda aka sani.

A wani bangaren na hirar kuma gwamna Uba Sani ya soki ’yan siyasar Kasar nan da ke sukar gwamnatin Shugaban Tinubu.
Acewar Uba Sani su na yin hakan ne domin neman mulki, inda ya ce ba su da wani abu da za su iya magance matsalolin Kasar nan.
