Gwamnatin tarayya ta kafa wani kwamti da zai bibiyi karin kudin kiran waya da data da aika sakonni da aka amince a yi da kaso 50.

An cimma matsayar haka ne yayin zama da kungiyaar kwadago da su ka shirya yin zanga-zanga a yau Talata.
A zaman da aka yi a ofishin salataren gwamnatin tarayya, gwamnatin ta ce za ta kafa babban kwamiti da zai duba anincewa da tsarin kara kudin da kamfanoni su ka hukata a yi.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta amince da yin karin kaso 50 na kudin kira, data da aika sakonni bayan da kamfanonin sadarwa su ka bukaci haka.

Kamfanonin sun bukaci a yi karin da kaso 100 sai dai gwamnatin ta amince a yi da kaso 50.
