Cibiyar yaƙi da ta’addanci ta Najeriya karkashin ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan sha’anin tsaron ƙasa ta ce an samu raguwar yin garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa da kaso 16.3 a shekarar 2024 da t gabata.

Mai sanya idanu a kan cibiyar Manjo Janar Adamu Garba Laka ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai yau Alhamis.
Ya ce an samu ragin aiknta garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa.

A cewarsa, jihohin Kaduna da Katsina da Zamfara su ne kan gaba wajen samun rahoton garkuwa da mutane.

Ya ce an samu raguwar aikata laifin ne sakamakon ayyukan da aka samu na ci gaba karkashin mai ba shugaban kasa shawara kan sha’anin tsaro Malam Nuhu Ribadu
Ƙididdigar ta ce an fi yin garkuwa a ƙauyuka sai birane makarantu da manyan hanyoyi.
A cewarsa, cibiyar za ta hada kai da gwamnonin jihohi don karfafawa al’umma ta yadda za su daina biyan kuɗin fansa.
Sannan a magance rashin aikin yi da sha’anin tattalin arziki
