Gwamnan Jihar Nasarawa Abdullahi Sule ya dakatar da dukkan mashawartanshi, hadimai na musamman da sauran wasu masu rike da mukamai a gwamnatinsa.

Gwamnan ya sallami jami’an gwamnatin nasa ne a yau Juma’a a yayin wani taron bankwana da su da ya gudanar a zauren Majalisar zartarwa da ke gidan gwamnatin Jihar.
Bayan dakatar da su gwamna Sule ya yaba musu bisa gudummawar da suka bai’wa gwamnatinsa, inda ya ce wasu daga cikinsu ka iya kara samun aiki a karkashin gwamnatinsa a wasu mukaman da zai nada a nan gaba.

A yayin taron gwamnan ya kuma rantsar da Barista Labaran Magaji a matsayin sabon sakataren gwamnatinsa, wanda na daya daga cikin kwamishinonin da gwamnan ya sallama daga bakin aiki, inda a baya shine Kwamishinan shari’a na Jihar.

Sannan gwamnan ya kuma rantsar da sabon shugaban yankin Udage da ke karamar hukumar Nasarawa Commodore Yahya Owuna mai ritaya, da kuma shugaban Kwalejin ilmi ta Akwanga da ‘yan Majalisar gudanarwa na Kwalejin.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya gwamnan Sule ya rushe majalisar zartarwar Jihar, tare da dakatar da dukkan kwamishinoninsa daga bakin aiki.
Idan kuma a halin yanzu ya aikewa da Majalisar dokokin Jihar sunayen mutane 16 don tabbatar da su a matsayin Kwamishinoni.
