Gwamnatin tarayyar Najeriya na shirin aiwatar da sabon tsarin karatu na 12-4 maimakin tsarin 6-3-3-4 da ake kai a yanzu.

Hakan na nuni da cewar karatun firamare shekara shida da ƙaramar sakandire shekara uku da babban sakandire shekara uku za su dunkule su koma shekara 12 a matsayin matakin farko na karatun dalibai.

Tsarin karatu na shekara 12 sai kuma karatun jami’a shekara huɗu.

Wannan na zuwa ne bayan da ministan ilimi Dakta Tunji Alausa ya buƙaci masu ruwa da tsaki a nangaren ilimi su duba yiwuwar haka.

Zaman da aka yi a jiya Alhamis an miƙa buƙatar amincewa da shekara 16 a matsayin mafi karancin shekaru da dalibi zai shiga manyan makarantu a ƙasar.

Taron da aka yi ya samu halartar kwamishinonin ilimi na jihohi 36 na Najeriya.

A cewar ministan, ayar da tsarin karatun sakadire zuwa maratu matakin farko zai taimaka dalibai su samu ilimi ba tare da samun tsaiko ba har zuwa shekara 16.

Sannan kuma zai rage yawan yara da su ke guduwa daga makaranta.

Haka kuma za a samu tsayayyen tsarin karatu na bai ɗaya tare da koyar da dalibai sana’o’in dogaro da kai.

A wani cigaban kuma gwamnatin ta musanta soke tsarin karatun firamare da ƙaramar sakandire da kuma babbar sakandire da ake yadawa cewa ta yi.

Mai magana da yawun ma’aikatar ilimi ta ƙasa Folashade Boriowo ce ta sanar da haka a yau.

Ta ce an miƙa buƙatar sauya tsarin ne amma ba a aiwatar da shi ba zuwa yanzu.

A cewar sanarwar ba a tabbatar tare da aiwatar da sabon tsarin kamar yadda wasu kafofin yaɗa labarai su ka bayyana ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: