Gwamnan jihar Zamfara Ahmad Dauda Lawal ya shaidawa bankin duniya cewa, gwamnatinsa ta na samun nasara akan ƴan ta’addan da su ka addabi jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne, yayin wata ziyara da gwamnan ya kai ofishin bankin na duniya a ranar Juma’ar da ta gabata a birnin tarayya Abuja.

Inda ya shaida cewa hare-haren ƴan ta’adda akan manyan hanyoyi da ƙauyukan jihar, yanzu haka su na shawo kan matsalar, da kuma gagarumar nasara, inda al’umma su ke ƙara samun nutsuwar yin rayuwarsu.

Ziyarar dai an yi ta ne domin sake ƙarfafa alaƙar haɗin kai, tsakanin gwamnatin jihar ta Zamfara da kuma bankin na duniya.

Gwamna Lawal ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta duƙufa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar, ta hanyar bayar da goyon baya da samar da kayan aiki ga hukumomin tsaro.

A nasa ɓangaren babban daraktan bankin duniyar a Najeriya Ndiame Diop, ya jinjinawa gwamna Ahmad Lawal, bisa ƙoƙarinsa na kawo sauyin da ya dace a jihar ta Zamfara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: