Shugaban kasa Muhammad Buhari ya tafi kasar Rasha don halartar

wani gagarumin taro, na kwana 3.
Taron dai anasa ran zai maida hankali ne kan fadada hanyoyin samar da tsaro, kasuwanci, tare da zuba hannun jari a fannonin kimiyya da fasahar kirkirar iskar gas.

A yayin taron ana sa ran Shugaban kasa Muhammad Buhari zai gana da Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin don kulla kyakkwar dangantakar samar da tsaro, kasuwanci da San ya hannun jari, kamar yadda babban Mai taimakawa Shugaban kasa akan kafafen yada labarai malam Garba Shehu ya bayyana.

Taron dai ya samu halartar shugabannin Afrika da dama.