Mai bai a shugaban ƙasa shawara kan sha’anin tsaro Malam Nuhu Ribadu ya ce bai taɓa tattaunawa da wani kan batun zaɓen shekarar 2031 mai zuwa ba.

Elrufai ya zargi Ribadu da gwamna Uba Sani na amfani da wasu ofisoshi don daƙile shirinsa a zaɓen shekarar 2031.
Ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talabiji na Arise jiya Litinin.

Sai dai da yake mayar da martani dangane da jifan kalamai da Elrufai ke yi masa Malam Nuhu Ribadu ya ce bai taba tattauna batun zaben shekarar 2031 da wani ba.

Sannan ba ya son tsoma baki a kan kalaman da Elrufai ke yi a kansa.
A sakamakon haka ya bukaceshi da ya sarara masa don samun damar sauke nauyin aikin da ke gabansa.
Elrufai ya ce Ribadu na taɗe dukkan yan siyasa domin yana da shirin fitowa takara a zaɓen shekarar 2031.
Sai dai Ribadun ya ce ba zai yi sa insa da Elrufai ba.
