Hukumar Ƙididdiga ta Kasa NBS ta bayyana cewa tattalin arzikin Najeriya ya habaka da kashi 3.84 cikin 100 a zango na 4 na shekarar 2024 da ta gabata.

A rahoton da NBS ta fitar a yau Talata, ta ce karuwar tattalin arzikin ta wuce da kashi 3.46 da aka samu a zango na 3 na shekarar ta 2024.
NBS ta kara da cewa alkaluma na zango na 4 na shekarar sun wuce kashi 3.46 cikin 100 da aka bayar da rahoton samu a zango na 4 na 2023.

Sanarwar ta ce Bangaren ayyuka ne ke kan gaba a bunƙasar tattalin arziki na zango na 4 a 2024, wanda ya karu da kashi 5.37 cikin 100 tare da bayar da gudunmawar kashi 57.38 cikin 100 na jimillar tattalin arzikin.

NBS ta ce a jimillar kididdigar shekarar ta 2024, tattalin arzikin Kasar nan ya haɓaka ne da kashi 3.40 idan aka kwatanta da kashi 2.74 a 2023.
