Shugabna Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da bincike dangane da hatsarin babbar motar da ya faru a Abuja.

Zuwa yanzu adadin mutanen da su ka mutu ya kai goma yayin da sama da 30 su ka jikkata.
Tinubu a wata sanarwa da hadiminsa Bayo Onanuga ya sanyawa hannu, ya ce shugaban ya bai wa hukumomin da su ke da alaka da hanya da su gudanar da bincike kan musabbabin hatsarin.

Sannan ya jajanta tare da yin taaziyya ga iyalan wadanda su ka rasa yan uwansu.

Babbar motar dai ta wace a babbar hanyar Abuja zuwa Nyanya zuwa Keffi kuma ta kama da wuta da wasu motoci.
Ana zargin cikin motocin da su ka kama da wuta har da wata motar dakon mai.
Motoci 14 ne su ka kone kamar yadda yan sanda su ka bayyana.
Hukumar kula da jini a Najeriya ta buƙaci al’umma musamman na birnin da su kai gudunmawar jini don taimakawa waɗanda lamarin ya shafa.