Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Godswill Akpabio ya musanta rade-raden da ke yawo cewa ya bai’wa Sanatocin Majalisar cin hancin dala 15,000 domin amincewa da bukatar shugaban Tinubu na ayyana dokar tabaci a Jihar Rivers.

Mai magana da yawun Akpabio, Hon Eseme Eyiboh ne ya musanta zargin da ake yiwa Akpabio na rabon Kudin.
Akpabio ya bayyana lamarin a matsayin wani bangaren na tsanar da ake yi masa tun bayan da ya hau kan kujerar shugabancin Majalisar.

Hakan na zuwa ne bayan bullar wata jita-jita da ke yiwa shugaban Majalisar na jagorantar rabon kudi a lokacin buda bakin azumi da ya shiryawa sanatoci a gidansa da ke Abuja.

Jita-jitar ta zargi shugaban Majalisar da raba dala 5,000 ga ‘yan uwansa Sanatoci a ranar Talatar da ta gabata, ya yin da daga bisa kuma ya sake kara musu dala 10,000 a ranar Larabar da ta gabata gabanin kada kuri’a kan ayyana dokar tabaci a Jihar Rivers.
Sanarwar ta bayyana cewa tun bayan samun shugabancin Majalisar dattawa da Sanata Akpabio ya yi ya yake shirya buda baki, ba sai a wanna karon ba.
Eyiboh ya bayyana cewa babu wani dalili da zai sanya shugaban Majalisar ya bai’wa sanatocin wadannan kudaden.
Ya ce mutane na yin hakan ne don bata masa suna, inda ya bukaci mutane da su yi watsi da jita-jitar.