Mayaƙan Boko Haram sun hallaka manyan jami’an soji biyu a ƙauyen Izge.

Ana zargin mayaƙan Boko Haram da kashe sojojin a ƙauyen Izge da ke ƙaramar hukumar Gwoza ta jihar Borno.

Lamarin ya faru daren wayewar yau Lahadi yayin da mayaƙan su ka zagaye sojojin.

Sanata Ali Ndume ya nuna kaɗuwarsa kan harin da aka kai kasancewarsa wanda ya taso a ƙaramar hukumar.

Harin da aka kai a ƙauyen Izge dai na zuwa ne makonni biyu bayan da mayaƙan su ka kai wa sojoji hari a ƙauyen Wulgo da ke ƙaramar hukumar Gamboru Ngala a jihar.

A harin da su ka kai sun hallaka sojoji da dama.

Jami’an sojin da aka hallaka akwai mai muƙamin Kaftin da kuma Kofur.

Leave a Reply

%d bloggers like this: