Babban sufeton ƴan sandan Najeriya Kayode Egbetokun ya janye sammacin da ya aikewa da sarki Muhammadu Sanusi ll.

A wata sanarwa da mai magana da yawun ƴan sandan Olumuyiwa Adejobi ya fitar, sufeton ya umarci sashen da ke bincike a kan zargin da ake yi wa sarkin kan su janye sammacin da su ka aike masa.


An yi sammacin Sarki Sanusi ll ne dai hayan zargin karya dokar da jami’an yan sanda su ka saka ta hana hawan sallah a bana.
Bayan sammacin da aka aikewa da sarkin mutane daban-daban na zargin hakan cin zarafi ne ga sarautar gargajiya musamman a arewacin ƙasar.
Sanarwar ta ce kafin sallah jami’an sun yi ƙoƙarin yin sasanci don ganin an dakatar da hawan sallar tsakanin sarakunan biyu.
Sai dai yan sanda sun zargi Sarki Sanusi ll da bijirewa dokar hana hawan da aka yi.
Jami’an sun ce sun janye sammacin da aka aike masa ne bayan tuntubar masu ruwa da tsaki da kuma neman shawararsu a kai.