Babbar kotun da ke zaman a garin Jos babban birnin Jihar Filato, ta sanya ranar 28 da 29 ga watan Mayun shekarar da muke ciki a matsayin ranar da za ta ci gaba da sauraron shar’ar kisan Manjo-Janar Idris Alkali mai ritaya.

A ranakun da kotun ta sanya domin ci gaba da shari’ar wadanda ake zargi da hannu a kisan za su fara gabatar da shaidunsu.
Kotun ta dage shari’ar ne bayan da bangaren masu shigar da kara suka gabatar da tambayoyinsu ga Manjo- Janar U.I Muhammad mai ritaya akan kisan Alkali.

Janar Alkali dai shine tsohon shugaban gudanarwar Rundanar sojin Kasan Najeriya, inda ya bace makwanni kalilan bayan yin ritarsa a aikin soja, a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Jihar Bauchi daga birnin Tarayya Abuja.

Alkali shi ne ke tuka motarsa a yayin tafiyar, bayan ya biya ta Jihar Filato.
A shekarar 2018 da ta gabata lokacin da Janar Alkali mai ritaya ya bace, Janar Muhammad shi ne Kwamandan runduna ta 3, ya yi da kuma yake jagorantar aikin neman kubtar da Alkali.
Janar Muhammad shi ne wanda ya jagoranci zurzurfan bincike akan batan Alkali har ta kai ga an gano motarsa a yankin Du, inda kuma daga bisa aka gano gawarsa a wata Tsohuwar rijiya a Kauyen Guchwet da ke yankin Shen a cikin karamar hukumar Jos ta Kudu a Jihar ta Filato.
Sai dai a zaman kotun na jiya Litini, lauyoyin da ke kare kai sun tambayi Janar Muhammad, tare da neman yi musu karin bayani, akan bayanan da aka bayar a baya tare da shaidunsa akan mutuwar Janar Alkali.
A yayin tambayoyin an shafi akalla sa’o’i biyu akansu, inda kuma suka mayar da hankali kan bayanan farko da ya bayar da kuma na baya akan kisan.
Bayan tattaunawa akan lamarin Akalin kotun mai shari’a Arum Ashom ya dade sauraran shari’ar zuwa watan Mayu, domin sauraron shaidu na gaba, da kuma masu kare kai su fara kare kansu.