Gwamnan Jihar Kaduna Malam Uba Sani ya bai’wa hukumar da ke kula da fansho ta Jihar umarnin fitar da Naira biliyan 3.8 don biyan tsofaffin Ma’aikatan Jihar wadanda suke raye da wadanda suka rasu hakkokinsu.

Babban Sakataren yada labaran gwamnan Uba Sani, Malan Ibrahim Musa ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Acewar Sanarwar ta ce gwamnatin Jihar ta bayar da umarnin sakin kudaden ne sakamakon amsa kiraye-kirayen sakin kudaden da tsofaffin ma’aikatan Jihar ke yi, da kuma iyalan ma’aikatan da suka rasa rayukansu.

Sanarwar ta kara da cewa aikin tantance ‘yan fanshon da gwamnatin Jihar ke yi, ta yi hakan ne domin gano ‘yan fansho na Bogi, don ganin an biya kudin fanshon na wata-wata ba tare da wani tasiko ba.

Sanarwar ta bayyana cewa gwamnatin Jihar ta daura damarar kula da walwala da jindadin tsofaffin Ma’aikatan, bisa gudummawar da suka bayar wajen ci gaban Jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: