‘Yan bindiga a Jihar Zamfara sun kaddamar da sabbin hare-haren ramuwar gayya a wasu Kauyuka da ke cikin karamar hukumar Tsafe, inda suka hallaka wasu mutane biyu, tare da yin garkuwa da wasu sama da 60 a hare-hare daban-daban suka kai Kauyukan.

Maharan sun yi wannan ta’asar ne domin yin ramuwa akan hallaka musu wasu daga cikin Jagororinsu da jami’an tsaro suka yi a makwannin suka shude.

Daga cikin jagororin ‘yan ta’addan da jami’an tsaro suka kashe sun hada da Kachalla Yellow da ake kira da Dan Isuhu, inda jami’an tsaron suka hallaka shi makwanni biyu da suka gabata, a lokacin da yayi yunkurin kai wani harin kwantan bauna kan Askarawan Zamfara.

Rahotannin sun nuna cewa an Kashe Isuhu Yellow ne tare da wani Dan uwansa, wanda ya kasance da a gurin Ado Aliero, da kuma wani shima shugaban ‘yan bindiga.

Tun bayan hallaka wadandan jagororin ‘yan ta’addan hare-haren Maharan da ake zaton yaran Ado Aliero ne ya kara karuwa a cikin Karamar hukumar ta Tsafe.

Harin baya-bayan nan da maharan suka kai a ranar Lahadi a Kauyen Gidan Arne, inda suka hallaka mutane uku, inda kuma mutane biyu suka mutu nan take, yayin aka kai dayan asibiti.

Mazauna yankin sun bayyana cewa ‘yan ta’addan sun yi garkuwa da akalla mata kimanin 40 a lokacin harin, yayin da aka kone gidaje da dama.

A ranar da wannan hari ya faru, shima wani harin na daban ya sake faaru a Kauyen Keta, wanda yayi sanadiyyar rasa ran mutum guda, tare da kone motoci 11, sannan suka kwace kayayyki bayan sun fasa shaguna da dama.

Wani shugaban mazauna yanki Tsafe wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da hare-haren, ya ce kuma ce an kai wasu makamantanshi a ƙauyukan Yan Doton Daji da Unguwan Chida.

Acewarsa mutane 21 aka yi garkuwa da su, inda aka sace mutane 11 a Yan Doton Daji, yayin da aka sace mutane Goma a Unguwan Chida, da ke kusa da garin Kucheri.

Leave a Reply

%d bloggers like this: