Gwamnatin jihar Sokoto ta tabbatar da bullar cutar sankarau guda 300 a wasu daga cikin ƙananan hukumomin jihar.

Kwamishinan lafiya na Jihar Dr Farouk Abubakar ne ya bayyana hakan a yau Juma’a, a yayin taron wayar da kan mutane na kwana ɗaya da Kungiyar raya unguwanni ta Jihar WDC, tare da hadin gwiwar ma’aikatar lafiya ta jihar da kuma hukumar kula da lafiya matakin farko ta jihar suka shirya.
A yayin taron kwamishinan bai bayyana adadin mutane da suka mutu ba a bayan kamuwa da cutar, tun daga watan Fabrairu da aka samu bullar ta.

Acewar Kwamishinan har yanzu mutane 16 na ci gaba da karbar magani a asibitoci, inda da kuma sauran aka sallame su.

A yayin jawaban shugabannin taron mai bayar da shawara na musamman kan harkokin kiwon lafiya matakin farko na jihar Dr Muhammad Bello Marnona, da babbar sakatariyar hukumar Dr Larai Aliyu Tambuwal, sun yaba da irin namijin kokarin shugabancin hukumar ta WDC.
Acewarsu za a iya yin rigakafin cutar ta sankarau, inda suka shawarci jama’a da su ziyarci dukkan cibiyoyin kiwon lafiya mafi kusa da su don ganin sun samu magungunan da ya dace a dukkan lokacin da suka samu matsala.
Ana shi jawabin shugaban yankin Malam Ya’u Muhammad Danda wanda mataimakinsa Alhaji Faruk Umar Garba ya wakilta ya yaba da taron.
Shima Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na lll wanda Hakimin Gagi, Alhaji Sani Umar Jabbi ya wakilta, ya yabawa gwamnan Jihar Ahmed Aliyu da kuma jagororin gwamnatin Jihar bisa kokarin da suke yi wajen ganin sun inganta lafiyar al’ummar Jihar.