Kungiyar NCAJ mai tabbatar da kare hakkin dan adam ta yi kira ga Shugaban Kasa Bola Tinubu da ya ayyana dokar tabaci a Jihar Zamfara.

Kungiyar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Juma’a.
Kungiyar ta bayyana cewa ayyana dokar ta bacin a Jihar ya zama wajibi sakamakon kara ta’azzarar matsalar rashin tsaro da sauran wasu manyan laifukan.

Sanarwar ta bayyana cewa halin da jihar Zamfara ke ciki ya wuce kwatance, inda kuma kungiyar ta zargi gwamnatin jihar da take doka.

Sanarwar ta kara da cewa Jihar Zamfara ka iya rasa damarmaki da dama sakamakon majalisar jihar ba ta aiki yadda ya kamata, tun bayan dakatar da wasu ‘yan majalisar Goma.
Har ila yau kungiyar ta ce an dakatar da ‘yan majalisar ne saboda bisa sukar gwamnatin Jihar bisa yadda take tafiyar da batun tsaro, inda ta nuna fargabar cewa nan gaba jihar na iya fadawa cikin mulkin kama karya.