Tsohon gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Elrufa’i ya bayyana cewa ziyarar da suka kai’wa tsohon shugaban Kasa Muhammad Buhari sun kai masa ne domin yi masa gaisuwar sallah.

Elrufa’i ya bayyana hakan ne a jiya Juma’a ta cikin wata wallafa da ya fitar, inda ya ce ziyarar da suka kai’wa Buhari bata da alaka da siyasa, ko kuma sha’anin zaben 2027 da ke tafe.

Tsohon gwamnan na Kaduna ya bukaci ‘yan adawa da kada su yi zargin wani abu kan ziyarar da suka kai’wa Buhari a gidan da ke Jihar Kaduna, duba da cewa babu wani da ya danganci bangaren siyasa a cikinta.

Acewar Malam Nasir Elrufa’i sun je gidan Buhari ne domin yi masa gaisuwar sallah, ba don wani abu da ya shafi bangaren siyasa.

Daga cikin wadanda suka kai’wa tsohon shugaban Kasar ziyara sun hada, tsohon mataimakin shugaban Kasa Alhaji Atiku Abubakar, da tsohon gwamnan na Kaduna Malam Nasir Elrufa’i, da tsohon gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal, da dai sauran wasu tsofaffin gwamnonin Kasar.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: