Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa duba da irin tarin arzikin da Allah ya yi wa ƙasar, babu wani dalili da zai sa ƴan ƙasar su dinga rayuwa cikin talauci.

Ya ce Allah ya bai’wa ƙasar tarin albarkatun ƙasa, sai dai ana fama sakamakon rashin tafiyar da arzikin yadda ya kamata.

Obasanjo ya yi waɗannan kalaman ne dai a wajen wata liyafar cin abinci a ƙarshen makon nan, wacce gwamnatin jihar Abia ta shirya don karramashi a gidan gwamnatin jihar da ke birnin Umuahia.

Ya kuma ƙara da cewa idan har an gaza tafikar da arzikin da Allah ya yi wa ƙasar nan, to babu ababen zargi face al’ummar ƙasar da suka gaza yin abinda ya dace.

Ya kuma ƙara da cewa idan za a samu gwamnoni a jihohi 18 su yi abinda ya kamata wajen sauke nauyin da ke kansu, to za a gina da kuma bunƙasa ƙasar nan.

Tsohon shugaban ƙasar ya kuma yabawa ƙoƙarin gwamnan jihar ta Abia Alex Otti na kawo cigaba jihar, sakamakon yabawa da ƙoƙarinsa da al’ummar jihar ke yi.

Obasanjo ya ce babbar damuwarsa yanzu ita ce ƴan Najeriya su kasance cikin jin daɗi da walwala daga kyakkyawan shugabanci, ba wai a dinga gaishe shi ko girmama shi ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: