Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci hukumomin gwamnati da su yi bincike akan haramtattun makarantun gaba da sikandire waɗanda su ke ba bisa ka’ida ba, domin tabbatar da an kulle su baki daya.

Shugaban ya yi umarnin ne ga hukumar kula da jam’i’oi ta ƙasa NUC, hukumar kula da makarantun fasaha NBTE, da kuma sauran hukumomi masu ruwa da tsaki a ɓangaren.

Ya kuma umarce su da su tabbatar da an dakatar da ayyukan makarantun bogin na dindindin, don kiyaye ɓangaren ilimi da nagartarsa daga hannun gurɓatattun makarantu.

Tinubu a ƙoƙarin tabbatar da yunƙurin gwamnatinsa na inganta bangaren na ilimi, ya yi gargaɗin cewa dole ne a tabbatar da cewa ingancin ɓangaren ilimi a ƙasar nan bai gurɓata ba.

Shugaban ya yi wannan umarnin ne jiya Asabar, a wajen taron yaye ɗalibai karo na 14 na jami’ar yin karatu daga gida ta NOUN a Abuja.

Shugaban wanda ya samu wakilcin babbar darakta a ɓangaren ilimin jam’i’oi Hajiya Rakiya Gambo Iliyasu, ya buƙaci jam’i’oin da su bijiro da sabbin ƙirƙire-ƙirƙire, dan tabbatar da cewa ɗaliban da ake yayewa sun zama nagartattu.

Ya kuma ƙara da da cewa yanzu a matakin ƙasashen duniya, an mayar da tattalin arziki zuwa kan tsarin ilimi kuma bai kamata a bar Najeriya a baya ba.

Ya kuma jaddada buƙatar ganin an dakatar da yawaitar jam’i’oi na bogi, da kuma sauran makarantun gaba da sikandire a faɗin ƙasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: