Jam’iyyar SDP ta Kasa ta yi kira ga shugaban Kasa Bola Tinubu da sauran shugabannin Kasar nan da su mayar da hankalinsu wajen magance matsalar rashin tsaro da ke kara ta’azzara a fadin Kasar nan a yankin Arewa da Kudu.

Jam’iyyar ta bayyana hakan ne ta bakin Sakataren yaɗa labaran ta na Ƙasa Araba Rufus Aiyenigba, ya fitar ta cikin wata sanarwa a jiya Juma’a.
SDP ta bayyana cewa a halin yanzu Najeriya ta koma tamkar wani filin mutu, inda ta ce yawaitar hallaka mutane da ake samu musamman a ‘yan kwanakin nan na matukar tayar da hali Kasar.

Jam’iyyar ta kara da cewa daga cikin kashe-kashen mutanen sun hada da kisan killa da aka yiwa mafarautan ƴan Jihar Kano a jihar Edo, da kuma hare-haren ’yan ta’adda da aka kai’wa al’ummomi sama da 100 a sassan daban-daban na jihar Filato.

Sakataren ya ce gwamnatin da ke mulki a Najeriya ta rasa dukkan wata hikima mai kyau, tare da gaza samar da wata hanya da za ta kawo karshen yawaitar kashe-kashe mutane.
Jam’iyyar ta gargadi shugabannin Kasar da su daina mayar da hankali akan zaben shekarar 2027, su mayar da hankali akan tabbatar da tsaro a fadin Kasar.