A yau Litinin ake sa ran mataimakin shugaban Najeriya Sanata Kashin Shettima zai kai ziyara jihar Filato bayan rikicin da ya kai ga rasa rayukan mutane sama da 100.

Ziyarar da zai kai domin jajantawa mutanen bayan hare-haren da yan bindiga su ka kai ƙananan hukumomin Bokkos da Bassa a jihar.

Ministan jin ƙai a Najeriya Dakta Nentawale Yilwatda cewar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarni ga mataimakin shugaban ƙasar don kai ziyarar.

Yayin ziyarar, mataimakin shugaban ƙasar zai gana da masu ruwa da tsaki kan lamarin.

Sakamakon hare-haren, mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan sha’anin tsaro da manyan hafsoshin tsaron kasar sun kai ziyara jihar

Haka kuma ministan tsaro da wasu jami’an gwamnati sun kai ziyarar.

Tsohon ministan tsaro a Najeriya Laftanal Janar Theophilus Danjuma ya bukaci yan Najeriya da su tashi domin kare kansu.

Hare-haren da aka kai ya sa shugaban ƙasa ya bayar da umarni domin ganin an gaggauta kawo karshen matsalar baki ɗaya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: