Wani mutum a Jihar Neja ya saki matarshi saki Uku, bayan da jami’an tsaron ‘yan sanda suka kamata a wani dakin Hotal, bayan sun kai sumame.

Magidancin ya saki matar tashi ne a ofishin ‘yan sandan, bayan bayyana masa kamata.

Guda daga cikin jami’an tsaron ya ce an kama matar, mutumin ne, a lokacin da suka kai wani samame maɓoyar dillalan miyagun ƙwayoyi, da sauran batagari a wasu otel-otel da ke garin Minna babban birnin Jihar.

Jami’in tsaron ya ce a binciken da jami’an ‘yan sandan suka gudanar, bayan kawo matar ofishin ne suka gano cewa matar aure ce, bayan ji daga ’yan uwan mutanen da aka kama.

Sai dai ya bayyana cewa bayan zuwan mijin matar Ofishin ‘yan sandan nan take ya yi mata saki uku.

Daga cikin mutanen da jami’an suka kama ciki harda mata a yayin sumamen.

Jami’in ya kara da cewa har yanzu jami’an ‘yan sandan na ci gaba da gudanar da bincike akan mutanen da aka kama.

Leave a Reply

%d bloggers like this: