Hukumar kula da aikin hajji ta Jihar Yobe ta ce gwamnatin Jihar na ci gaba da shiryoyin hanyoyin da za su samarwar da maniyyatan Jihar kayayyaki domin sauƙaƙa musu wajen tafiya aikin hajjin bana.

Shugaban hukumar shugaban hukumar Alhaji Mai Aliyu Usman ne ya tabbatar da hakan a gurin wani taro da hukumar ta shirya don samar da hanyar saukakawa maniyatan Jihar da kuma jindadinsu.
Shugaban ya ce daga cikin abubuwan da hukumar ke shiryawa maniyan sun hada da samar musu da jakunkuna, kayan sawa na maza da mata da kuma lambar tantancewa da sauransu.

Acewarsa tabbatar da walwala da jindadin maniyatan Jihar da kuma ba su tallafi, hakan na daga cikin kokarin gwamnatin Jihar na ganin tabbatar da jindadi maniyyatan Jihar a lokacin aikin hajjin na bana da ke tafe.

A yayin taron shugaban hukumar, da kuma mambobin kwamitin Hajji na Jihar sun karɓi allurar rigakafin da ma’aikatan aikin hajji suka gudanar, don tabbatar da lafiya ga dukkan jami’an hukumar da kuma maniyyata.