Gwamnan jihar Katsina Umaru Dikko Radda ya jaddada aniyar gwamnatinsa wajen yin haɗin guiwa da wata gidauniya daga ƙasar Belgium mai suna REVIVE Foundation, wajen bunƙasa harkar lafiya a jihar.

Gwamnan ya bayar da tabbacin ne yayin karɓar baƙuncin wakilai daga gidauniyar, yayin wata ziyara da su ka kai masa ofishinsa a Katsina.

Gwamna Radda ya kuma nuna matukar godiyarsa game da ƙwarewar gidauniyar da goyon bayansu, sakamakon zaɓar yin haɗin guiwa da su ka yi da gwamnatin jihar wajen kawo wa al’umma sauki da farin ciki.

Gwamnan ya ce a shirye su ke su bayar da cikakken haɗin kai da samar da duk abinda ake buƙata, da zai basu damar yin aiki cikin kwanciyar hankali da nutsuwa.

A nata bangaren Shugabar gidauniyar Maimuna Bello ta bayyana cewa sun shafe sama da shekaru 11 su na ayyukansu a ƙasashe 8 da ke nahiyar Afirka, inda su ke bayar da gudunmawa a ɓangaren samar da ingantacciyar lafiya.

Ta ce kuma sun zaɓi zuwa jihar Katsina ne a wannan karon don su duba manyan asibitocin jihar, kuma sun yi komai cikin nasara inda su ka ziyarci asibitoci uku, kuma sun samu kyakkyawar tarba a ko ina.

Leave a Reply

%d bloggers like this: