Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni ya bayyana cewa rashin ilmi, da Talauci da ke addabar matasa ne ya sanya suke zama mayakan Boko-haram a yankin Arewa maso Gabashin Kasar nan.

Buni ya bayyana hakan ne a jiya Litinin a yayin wata ziyara da daliban cibiyar nazarin harkokin tsaro NISS suka kai masa ziyara.

Gwamnan wanda sakataren gwamnatin Jihar Baba Malam Wali ya wakila a yayin ziyarar, ya ce dumbin rashin ilmi da talauci ne suka taka muhimmiyar rawa wajen ƙara ƙarfafa ayyukan ‘yan ta’addan a yankin.

Kazalika gwamnan Buni ya ce ya zama wajibi a lalubo tushen magance matsalolin domin ganin an samu nasarar kawo kashen ta’addancin Kasar, inda ya yi gargaɗi da cewa gazawa a bangaren hakan zai ci gaba da kawo nakasu a dukkan bangarori.

Gwamnan ya kuma sake tabbatar da ƙudirin gwamnatinsa na yaƙi da rashin ilmi da talauci, ta hanyoyin shirye-shiryen ƙarfafa tattalin arziƙi, sake gina makarantun da suka lalace, da kuma ɗaukar sababbin malamai domin inganta fannin ilimi a jihar.

Sannan gwamnan ya bayyana muhimmancin tsayawa tsayin daka wajen ganin an magance kalubalan ‘yan ta’addan a yankin na Arewa maso gabas.

Gwamnan ya ce rashin daukar tsatstsauran mataki a kai hakan ka iya ci gaba da zama barazana ga ci gaban Kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: