Gwamnatin jihar Bauchi ta ƙaddamar da wani kwamiti da zai gano hanyar magance rikicin manoma da makiyaya a jihar

An ƙaddamar da kwamitin a ma’aikatar ƙananan hukumomi ta jihar.

Alhaji Hashimu Yakubu ne ya wakilci gwamna Bala Mohammed a wajen kaddamar da kwamitin

An ƙaddamar da shi ne ganin yadda ake asarar rayuka da dukiyoyi sakamakon rikicin da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.

Kwamitin zai kuma yi aikin sa ido a kan kai kawon makiyaya tare da wayar da kan manoma da makiyayan wahen warware matsaloli d kuma zaman lafiya.

Gwamna Bala Muhammad ya bukaci kwamitin da su mayar da hankali wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: