Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya yi alhinin sabbin hare-haren da aka kai jihar sa a kwanakin nan.

A wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaransa Daud Iliya ya sanyawa hannu yau Talata, ya ce gwamnatinsa na aiki kafada da kafada da gwamnatin tarayya, sojoji da sauran jami’an tsaro don tunkarar kalubalen tsaron.
Gwamna Zulum ya ce hare-haren da aka kai wa soji a kwanan nan abin akwai taɓa zuciya wanda ya buƙaci al’ummar jihar da su jar ba da hadin kai da kuma addu’a.

Haka kuma ya mika jajensa ga iyalan wadana su ka taka nakiya a a babbar hanyar Damboa zuwa Maiduguri.

Ya ce dukkan ta’addancin da aka yi abin alawadai ne.
Daga ciki akwai rasa rayukan sojoji, malain makaranta, da kuma fararen hula da ba su ji ba su gani ba.
Gwamna Zulum ya ce zai ci gaba da aiki da jami’an tsaro don tabbatar da cewar ba a ci gaba da samun faruwar haka ba a nan gaba.