Gwamnatin Jihar Kano ta musanta jita-jitar cewa ta sake karbo sabon bashi dala miliyan 6.6.

Musantawar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da darakta janar na hukumar kula da basassuka ta Kano Hamisu Sidi Ali ya fitar a jiya Alhamis.

Acewar sanarwar babu wani sabon bashi da hukumar ta karbo daga watan Yuni zuwa Disamban shekarar 2023 da ta gabata.

Gwamnatin na wannaan kalami ne sakamakon wasu zarge-zarge da kungiyar APC Patriotic Volunteers, bisa jagorancin tsohon Sakataren gwamnatin Kano Alhaji Usman Alhaji yayi.

Sanarwar ta ce ko kadan babu kamshin gaskiya a cikin jita-jitar, inda kuma ta soki tsohon sakataren gwamnatin kuma shugaban kungiyar kan zarge-zargen da ya yiwa hukumar.

Sanarwar ta kara da cewa ko kadan toshon sakataren bai san dokokin hukumar ba, inda ya bukaci da su fito fili su bayyana hujjojinsu akan zarge-zargen da suke yi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: