Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya nesanta kanshi daga wasu sakon ni da ake yadawa a kafafan sada zumunta ce yana shirin tsayawa takarar shugaban Kasa a yayin zaben shekarar 2027 da ke tafe.

Mai magana da yawun tsohon shugaban Ikechukwu Eze ne ya musanta batun a jiya Juma’a ga jaridar The Chable.

Wannan dai na zuwa ne bayan bullar wani sakon a kafar sadarwa ta Istagram a shafi dauke da sunan tsohon shugaban na Najeriya Jonathan, inda ya ke yin suka ga shugaba Bola Tinubu.

Wallafa ta kuma bayanna cewa shugabanni yanzu ba su da wani kuzari wajen gudanar da ayyukan, a don haka ya bukaci ‘yan Najeriya da su zabi shugabanci nagari a 2027 mai zuwa.

To sai dai Eze ya ce gaba dayan sakon babu gaskiya a cikinsa, yana mai cewa Jonathan bashi da shafi a kafar sadarwa ta Istagram.

Ya bukaci mutane da su yi watsi da sakon da ko kadan babu gaskiya a cikinsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: