Shugaban Majalisar dattawa Sanata Godswill Akpabio ya bayyana jam’iyyun adawa a Najeriya, ba za su taba iya hada kai guri guda ba, idan suka ci gaba da sukar gwamnatin shugaba Bola Tinubu.

Sanata Akpabio ya bayyana hakan ne a gurin kaddamar da wani titi a birnin tarayya Abuja, a ranar juma’ar nan.

Shugaban Majalisar ya bukaci da jam’iyyun adawa su daidaita kansu kafin zaben shekarar 2027 da ke tafe, yana mai cewa kada su zo su na zargin jam’iyyar APC ce ta hana rawar gaban hantsi.

Acewarsa shugaban Kasa Bola Tinubu baya fatan ganin Najeriya ta koma tsarin jam’iyya daya, inda kuma yake fatan ganin jam’iyyun Kasar sun magance matsalilin da ke addabar su.

Daga cikin Manyan ‘yan adawar da suka halarci kaddamar da titin sun hada da tsohon gwamnan Jihar Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi, da tsohon gwamnan jihar Ekiti Ayo Fayose.

Leave a Reply

%d bloggers like this: