Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta bayar da belin Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya a Majalisar dattawa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan akan kudi Naira miliyan 50.

Kotun karkashin jagorancin Mai Shari’a Chizoba Orji, ta kuma yi watsi da bukatar gwamnatin Tarayya akan wacce ake karar kan cewa a daureta a gidan ajiya da gyaran har zuwa lokacin da za a yanke mata hukunci.
Kotun ta ce babu wani dalilin da zai sanya ki amince da bayar da beli Sanata Natasha, tana mai cewa akwai hujjojin da ke bayyana cewa a shirye take ta fuskanci shari’ar.

Bayan kudin Belin Naira miliyan 50 kotun ta kuma bai’wa Sanatar umarnin gabatar mata da wanda zai tsaya mata a yayin shari’ar, inda kotun ta bukaci gabatar mata da mutum mai kima kuma ya ke da kadara a birnin Tarayya Abuja.

Acewar kotun ta yi amfani da tanaden sashe na 36 na kundin tsarin mulkin Ƙasa na shekarar 1999 da kuma sashe na 163 da 165 na kundin manyan laifuffuka na shekarar 2015.
Bayan haka ne kuma kotun ta dage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 23 ga watan Satumban shekarar nan ta 2025.