Hukumar jindadin Alhazai ta Ƙasa NAHCON ta bayyana cewa za ta kammala kwaso Alhazan Najeriya daga Ƙasa mai tsarki a ranar 28 ga watan Yunin da muke ciki.

Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Fatima Sanda Usara ta fitar.

Sanrwar ta ce alhazan Najeriya 6,528 ne suka dawo gida, inda Kamfanin Max Air ya kammala jigilar kwaso Alhazan sa a ranar Talatar da ta gabata.

NAHCON ta kara da cewa a halin yanzu hukumar ta Kasa da na sauran Jihohi, da kamfanonin jirage na yin aiki tukuru domin ganin an ƙarasa kwaso alhazan akan lokaci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: