Fadar shugaban Kasa ta bayyana cewa a halin yanzu shugaban Kasa Bola Tinubu ba zai ayyana wanda zai yi masa takarar mataimakin shugaban Kasa ba a zaben shekarar 2027, sai bayan babban taron jam’iyyar APC na Kasa na shekarar 2026.

Mai magana da yawun shugaban Bayo Onanuga ne bayyana hakan a jiya Alhamis ta hirarsa da Jaridar Daily Trust.
Onanuga ya bayyana cewa ba gaskiya ba ne yadda ake yada cewa shugaba Tinubu na shirin sauya mataimakinsa a zaben mai zuwa, duba da yadda ‘yan jam’iyyar ke goyan bayan Tinubu shi kadai ba tare da Kashim Shettima ba.

Kazalika Onanuga ya kara da cewa idan aka yi duba da tsarin mulkin Kasa, za a ga cewa da farko sai an fara zaben dan takarar kafin daga bisani kuma ya zabe wanda zai yi masa mataimaki, yana mai cewa hakan ne ya faru ma a lokacin tsohon shugaban Kasa Muhammad Buhari sai da aka fara zabensa sannan ya zabi wanda zai yi masa taimaki.

Acewarsa daga lokacin da hukumar INEC ta fitar da jadawalin zabukan jam’iyyu za ta shirya babban taronta, inda anan za a tsayar da shugaban kasa, shi kuma ya zabi mataimakinsa.
Ya kara da cewa babu rashin jituwa tsakanin shugaba Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima, yana mai cewa babu kamshin gaskiya a cikin rade-radin da ake yadawa.