Daga Ummahani Abdullahi

Shugaban hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano, KAROTA, Hon Faisal Mahmud Kabir ya ce hukumar za ta ci gaba da yin aiki kafaɗa-da-kafaɗa da ƙungiyar masu fasahar kafar sadarwa don tattara bayanai na babura masu kafa uku da sauran ababen hawa da ke aiki a fadin jihar Kano.

 

Shugaban ya bayyana haka ne a jiya Laraba a lokacin da mambobin kungiyar masu gudanar da fasahar sadarwa suka kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa.

 

Faisal Mahmud Kabir wanda ya jaddada mahimmancin masu amfani da yanar gizo wajen bunƙasa tattalin arzikin kasa, inda ya tabbatar wa da ƴan ƙungiyar cewa hukumar Karota za ta haɗa kai da da masu gudanar da ayyukan ta wannan hanyar.

 

Tun da farko, shugaban kungiyar, Kwamared Abubakar Sani ya ce mambobin ƙungiyar sun kai ziyara helkwatar Karota domin neman goyon bayan Hukumar wajen gudanar da ayyukansu.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: