Ministar Al’adu Hannatu Musawa ta bayyana matsayarta akan yankin da ya fi dacewa shugaban Ƙasa ya fito daga ciki.

Musawa ta ce yankin kudancin Kasar nan ne ya fi dacewa da ya ci gaba da kasancewa rike da Kasar domin samun adalci da daidaito a Najeriya.
Acewarta duk da kundin tsarin mulkin Kasa bai wajabta tsarin karɓa-karɓa ba, amma manyan jam’iyyun siyasa suna bin tsarin sauya mulki tsakanin Arewa da Kudu.

Musawa ta bayyana hakan ne a yayin wata fira da aka yi da ita a gidan talabijin na Channels a yau Juma’a.

Ministar ta bayyana cewa tun da an samu Shugaba daga yankin Arewa wato tsohon shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi mulki har wa’adi biyu to babu shakka yafi dace a barwa yankin Kudu shima yayi wa’adi biyu hakan shi zai fi zamowa adalci.