Mataimakin shugaban Kasa Sanata Kashim Shettima ya musanta Zargin da ake yi masa na Caccakar shugaba Tinubu, yana mai cewa an wulakanta Maganganunsa.

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya bayyana cewa ba ya caccakar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa an fassara kalamansa ba daidai ba a wani rahoto da ke yawo a kafafen sada zumunta da wasu gidajen jaridu.

Shettima ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da kakakinsa, Stanley Nkwocha ya fitar a ranar Alhamis.

Shettima ya ce kalaman da ya yi a wani taro na kasuwanci a Abuja an yanke su daga cikakkiyar ma’anarsu kuma an fassara su ta wata hanya mai nuni da kiyayya ko rashin jituwa tsakaninsa da Shugaban ƙasa Bola Tinubu.

Sanarwar ta kara da cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa ya tsaya tsayin daka wajen goyon bayan manufofi da shirye-shiryen Shugaba Tinubu tun kafin zaɓe har zuwa yau.

 

Sannan kuma bai taɓa yin wata magana da za ta zubar da mutuncin shugaban ƙasa ba.

Shettima ya ƙara da cewa kalamansa sun ta’allaka ne kan irin gudummawar da kowane yanki na ƙasa ke bayarwa wajen gina sabuwar Najeriya, ba wai suka ba ne kan Shugaba Tinubu ko manufofinsa.

Ya bukaci ‘yan Najeriya da su guji yada labaran marasa gaskiya da ka iya haddasa rashin jituwa ko rikici a cikin gwamnati da tsakanin jama’a.

Leave a Reply

%d bloggers like this: