Kamfanin mai mai zaman kansa na Najeriya NNPC na duba yiwuwar cefanar da matatun mai da yake da su.

Shugaban kamfanin Bashir Bayo Ojulari ne ya bayyana haka.


Matatun guda uku na Warri, Fatakwal da Kaduna ne ke ƙarƙashin kamfanin.
Kafin wannan furuci, Alhaji Aliko Dangote ya ce ba lallai bane matatun man su dawo aiki kamar yadda ake tsammani bayan lashe aƙalla dala biliyan 18.
Ojulari ya bayyana haka a ƙasar Austria yayin wata ganawa da aka yi da shi a gidan talabiji na Bloomberg.
Ya ce tsawo lokaci da aka shafe ana kashewa matatun kuɗi da nufin gyarasu ba sa samar da kyakkyawan sakamakon da za a iya ci gaba da riƙe su.
A cewarsa su na kan bibiya da kuma duba yiwuwar cefanar da matatun matuƙar ba za a samu abinda ake so a kansu ba.
A lokacin tsohon shugaban kamfanin NNPC Malam Mele Kyari aka buɗe tare da dawo da matatun mai na Warri da Fatakwal wanda su ka koma aiki babu ƙaƙƙautawa.
Sai dai bayan sauya shugaban kamfanin wanda shugaba Bola Ahmed Tinubu matatun su ka sake tsayawa wanda ake zargin kamfanin ba zai iya ci gaba da kulawa da su a ƙarƙashinsa ba.