Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirin daukar ma’aikatan lafiya guda 70,000 nan da shekarar 2029 domin karfafa tsarin kula da lafiyar al’umma da kuma saukaka samun lafiya a yankunan da ba su da isassun asibitoci.

Daraktan Hukumar Raya Asibitocin Sha-ka-tafi na Kasa (NPHCDA), Dr. Muyi Aina, ne ya bayyana hakan a wani taro na Nahiyar Afrika da aka gudanar a Abuja, wanda cibiyar Africa CDC da UNICEF suka shirya don tattauna batutuwan da suka shafi lafiyar al’umma da tsare-tsaren samar da ma’aikatan lafiya a matakin ƙasa da ƙasa.

Dr. Aina ya bayyana cewa an tsara shirin ne domin samar da ma’aikacin Lafiya ɗaya ga kowanne gida 250, domin a kai ga samun wadatacciyar hidima ga ‘yan Najeriya sama da miliyan 160.

Wadannan ma’aikatan za su rika bayar da rigakafi, wayar da kai, sa ido kan yaduwar cututtuka da kuma gina aminci da fahimtar da al’umma game da tsarin kula da lafiyarsu.

Ya kuma ce shirin zai ba da horo, kayan aiki da kayan taimako na zamani domin tabbatar da ingantaccen aiki, inda yanzu haka jihohi takwas suka amince da tsarin, ciki har da Bauchi, Borno, Kaduna, Yobe, da Zamfara.

A nata bangaren, wakiliyar UNICEF a Najeriya, Ms. Wafaa Saeed Abdelatef, ta jaddada goyon bayan kungiyar ga tsarin kiwon lafiya na al’umma a matsayin hanya mafi tasiri don kai hidima ga yara da ba a kai ga musu rigakafi ba.

Ta ce samun karin jari daga cikin gida da waje zai taimaka wajen cimma burin kungiyar Tarayyar Afirka na daukar ma’aikatan lafiya miliyan biyu kafin 2030.

Haka kuma, shugabannin Africa CDC sun ce ma’aikatan lafiya na unguwanni su ne ginshikin samun kulawar lafiya ta kowa da kowa, kuma za su ci gaba da aiki tare da gwamnatocin kasashe domin tabbatar da cewa ba a bar wata al’umma a baya ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: