Ministan babban birnin tarayya Nyesome Wike ya ja hankalin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan akan zaɓen 2027 da ke tafe.

Ministan ya bai wa tsohon shugaban ƙasar shawarar kada ya fito takarar shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2027 da ke tafe tare da nuna masa cewa ya riƙe mutuncin shi a matsayin shi na babban mutum.
Shawarar na zuwa ne a dai dai lokacin da ake zargin tsohon shugaban ƙasar ya ke shirin sake fitowa takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin jam’iyyar PDP duk da haka dai bai ce komai a kai ba.

Wike ya bayar da shawara ne yayin wata tattaunawa da sukayi da ƴan jarida a Abuja ranar Litinin.

Ya ce ya San Jonathan sosai kuma ya na jin daɗin yadda ya ke a matsayin sa na babban mutum ya na fatan ci gaba da zama a haka.
Ministan ya yi zargin wasu a cikin jam’iyyar na ƙulla hanyar da tsohon shugaban ƙasar don sake fitowa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 da ke tafe.
Ya ce wadanda su ke kiran takarar Jonathan su ne ƴan siyasar da su ka yi amfani da shi a shekarar 2015 da ta gabata.
Wike ya ja hankalin yan jam’iyyar PDP akan yanke hukunci da zai ta’azzara matsala dajam’iyyar ke fuskanta.
Ya ce shi bazai fito takara ba domin ya na da kima da tarbiyya, domin babu yadda za a ce wanda ya goyi baya na neman takarar shugaban ƙasa kuma shi ma ya fito takara.
