Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya sanar da kawo ƙarshen dokar ta-baci da aka sanya a Jihar Rivers tun a ranar 18 ga Maris, 2025.

A cikin jawabin da ya gabatar daga fadar shugaban ƙasa, Tinubu ya ce an kafa dokar ta-bacin ne sakamakon rikicin siyasa da ya yi ƙamari tsakanin Gwamnan jihar, Siminalayi Fubara, da ’yan majalisar dokokin jihar.

Shugaban ya bayyana cewa rikicin ya kai ga gaza gudanar da harkokin gwamnati, inda aka samu rarrabuwar kawuna tsakanin ’yan majalisar, guda huɗu na goyon bayan gwamna yayin da sauran 27 ke goyon bayan kakakin majalisar.

Ya ce hakan ya hana gabatar da kasafin kuɗi, abin da ya haddasa durƙushewar gwamnati gaba ɗaya, lamarin da Kotun Koli ta tabbatar da shi a hukuncinta, inda ta bayyana cewa babu gwamnati a Rivers State.

Tinubu ya ce duk da ƙoƙarinsa da na wasu ’yan Najeriya don shawo kan rikicin, bangarorin biyu sun ƙi sasantawa, lamarin da ya tilasta shi amfani da sashe na 305 na kundin tsarin mulkin 1999 wajen kafa dokar ta-baci.

“Idan ban ɗauki wannan mataki ba a lokacin da aka kai ga mummunan halin da gwamnati ta gaza aiki, to da na gaza wajen kare zaman lafiya da tsaron jama’a,” in ji Shugaba Tinubu.

Ya kuma gode wa majalisar dokokin tarayya, sarakunan gargajiya da jama’ar Rivers bisa goyon bayan da suka bayar yayin dokar ta-bacin.

Shugaban ya ce bayan samun sabon yanayi na fahimtar juna da shirye-shiryen komawa ga tsarin dimokuraɗiyya, ba bu dalilin ci gaba da dokar ta-bacin bayan cikar watanni shida.

Saboda haka, daga misalin ƙarfe 12 na daren 17 ga Satumba, 2025, dokar ta-bacin ta ƙare. Gwamna Fubara, mataimakiyarsa Ngozi Nma Odu, da kakakin majalisar, Martins Amaewhule, tare da ’yan majalisar za su koma bakin aiki daga ranar 18 ga Satumba, 2025.

Shugaba Tinubu ya yi amfani da damar wajen tunatar da sauran gwamnonin jihohi da majalisun dokoki cewa zaman lafiya da kyakkyawan shugabanci su ne tushen kawo romon dimokuraɗiyya ga ’yan ƙasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: