Hukumar dakile cutuka masu yaduwa a Najeriya NCDC ta tabbatar da cewa zazzabin Lassa ya yi sanadiyar mutuwar mutane 168 a cikin jihohi 21 na Najeriya a shekarar nan ta 2025.

A cikin rahoton ta na mako na 38, hukumar ta bayyana jimillar mutane 4,543 da ake zargi da kamuwa da cutar, wanda 897 aka tabbatar da ba sa dauke da cutar, tare da adadin wadanda suka mutu ya kai kashi 18.7 cikin dari.
NCDC ta bayyana cewa jihohi hudu da suka hada da Ondo, Edo, Taraba, da Bauchi, su ne Jihohin da cutar ta bulla, wanda ya kai kashi 67 cikin 100 na duk wadanda aka tabbatar da kamu da cutar, inda ta ce Jihar Ondo kadai ce ta fi kowacce, sai kuma Edo da Bauchi.

Sauran jihohin da abin ya shafa sun hada da Ebonyi, Benue, Kogi, Gombe, Plateau, Kaduna, Nasarawa, Enugu, Delta, Anambra, Rivers, Borno, Oyo, Ogun, Legas da kuma babban birnin tarayya.

Rahoton ya kuma yi nuni da cewa, mafiya yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar ƴan shekaru 21 zuwa 40, inda maza da mata suka kamu da cutar.
Hukumar ta ce wannan rukunin shekaru ne suka fi kowa ma’amala a fannin zamantakewa, wanda hakan ya sanya suka fi kamuwa da cutar ta lasa.