Gidauniyar Down syndrome a Najeriya ta bukaci shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu da gwamnatin tarayya da su gaggauta aiwatar da dokokin masu bukata ta musamman da aka riga aka kafa a fadin kasar domin tabbatar da tsaro, ingantaccen kiwon lafiya, hada kai, da kuma ba su cikakkiyar kulawa ta musamman.

An gabatar da bukatar hakan a yau Asabar ta cikin wata sanarwa da aka rabawa manema Labarai, yayin da gidauniyar ta ke gudanar da taron da ta saba yi duk shekara a kowacce ranar 24 ga watan oktoba, mai taken kulawa da lafiyarsu.

An shirya taron domin jan hankali, wayar da kai da kuma bayar da taimako a sakateriyar karamar hukumar Ikeja da gidauniyar Nigeria sovereign investment Authority da gidauniyar 7 fifteen philanthropic su ka dauki nauyi.

A cikin sanarwar gidauniyar ta jaddada cewa ci gaba da bayar da shawarwarin na ta ya samo asali ne daga karuwar gibin da ake samu a cikin al’umma, musamman ga masu bukata ta musamman, wadanda ba su da damar iya fitowa suyi magana.

Acewarta idan suka yi magana game da nakasa, wasu mutane na iya yin magana don kwato musu hakkinsu, yayin da wasu kuma ba za su iya ba, wanda hakan ya sanya suke yin magana da yawunsu.

Gidauniyar ta bayyana damuwarta kan yadda ba a bai’wa masu bukata ta musamman kulawa a cikin tsarin kiwon lafiyar kasar, wanda ya janyo kalubalen rashin bayar da kariya a lafiyar su.

Gidauniyar ta bukaci gwamnati da ta gina tsare-tsaren kula da lafiya masu dorewa don magance waɗannan matsalolin.

Da take karin haske kan shirye-shiryen da ta ke ci gaba da yi, Gidauniyar ta bayyana cewa samar da ilimi, kiwon lafiya, da koyar da sana’o’in hannu ta cibiyar su da ke Legas, yayin da suke koyor da sana’o’in aski, gyaran gashi, biredi, kere-kere, da sana’ar leda, a karkashin takardar shedar Hukumar Ilimin Fasaha ta Jihar Legas.

Bugu da kari ta ce Waɗannan shirye-shiryen, gami da shirin noman kifi da aka tsara, kuma an samar da su ne don haɓaka ‘yancin kai, dogaro da kai a tsakanin masu bukata ta musamman.

Kazalika gidauniyar ta ce idan gwamnatin shugaba Tinubu ta tabbatar da dokar a Najeriya za ta kasance gaba wajen ci gaban kasar da ma masu bukata ta msaumman baki daya.

Taron ya kuma janyo hankalin hadin gwiwar wasu kungiyoyi irin su pacelli, gidauniyar punuka,gidauniyar OCD lady Atinuke.

Har ila yau sanarwar ta bayyana cewa a ranar 8 ga watan Augusta da 17 daga cikin jihohin 36 a Najeriya na shirin shigar da dokar masu bukatar ta musamman ta kwakwalwa.

Ta ce da zarar Jihohi 19 daga cikin 36 sun shigar da dokar za ta fara aiki kuma nan ba da jimawa ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: