Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani, ya amince da fitar da naira biliyan 2.321, domin biyan kudaden fansho, da garatuti ga wadanda suka yi ritaya na iyalan ma’aikatan gwamnati da suka rasu a fadin jihar.

Bayar da kuɗin ya ƙunshi haƙƙoƙin tarawa a ƙarƙashin Tsarin bayar da gudunmawa na Fansho na CPS, da na garatuti ƙarƙashin tsarin DBS.

Idan gwamnatin Jihar ta biya wadanan kudaden, jihar ta biya naira biliyan 6.678 a shekarar 2025, jimillar naira biliyan 13.5 a cikin shekaru biyu da gwamnatin Uba Sani ta yi.

Kwamishinan yada labarai na Jihar Ahmed Maiyaki, ya ce jin dadin ’yan fansho shi ne babban abin da gwamnatin ta sanya a gaba, yana mai jaddada cewa za a ci gaba da biyan kudaden da ake biya a kan lokaci don saukakawa manyan.

Acewar Sakataren Zartarwa na ofishinhukumat Fansho a Jihar, Ibrahim Balarabe, ya ce wannan rukunin na baya-bayan nan zai amfanar da ma’aikata 661 da suka yi ritaya, da iyalan wadanda suka mutu a fadin Kananan Hukumomin Jihar, tare da naira biliyan 1.736, don Tallafawa Ma’aikata 511 da suka yi ritaya a karkashin Hukumar CPS, da kuma naira miliyan 585, don biyan garatuti na wadanda suka mutu 315 da ’yan fansho a karkashin DBS.

Sakataren ya ce ga wadanda ke karkashin shirin bayar da gudunmawar fansho, za a ba su hakkinsu kai tsaye zuwa asusun ajiyarsu, yayin da nan ba da dadewa ba za a gayyaci ‘yan fanshon, don tantancewa da kafin biyasu.

Ya ce amincewar na kara jaddada kudirin gwamnatin na tabbatar da walwala ga ‘yan fansho, da ba su hakkokinsu, da kuma karfafa amincewar ma’aikatan Jihar ta Kaduna.

Leave a Reply

%d bloggers like this: