Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya tabbatar da cigaba da bada haɗin kai a bisa dukkanin bayanan da kwamitin binvike kan tabbatar da shirin ba da ilimi kyauta kuma dole a jihar kano.

A yayin wani zaman tattaunawa da gwamnan ya yi da masu ruwa da tsaki a harkar ilimi, ciki har da shugaban makarantun firamare da sakandire, gwamnan ya tabbatar da cewar Samar da ilimi kyauta kuma ɗole a Kano zai ƙunshi jin daɗin ɗaliban jihar.

Cikin shirin da gwamnatin ke yi na tabbatar da jin daɗi da walwalar ɗalibai kyauta, akwai samar da motoci zirga zirga tare da samar da wuraren zama a makarantu.

Shugaban kwamishin Dakta Kabiru Shehu ya tabbatarwa da gwamnan cewar, dukkanin mambobin kwamitin na aiki tuƙuru don tabbatar da nasarar shirin.