Hedikwatar Tsaron Najeriya Ta Karyata Zargin Yunƙurin Juyin Mulki.

A wani jawabi da ta fitar don fayyace dalilin soke bukukuwan samun ‘Yancin Kai, Hedikwatar Tsaron Najeriya ta musanta jita-jitar da ke yawo kan zargin yunƙurin juyin mulki.

A cikin wata sanarwa da Birgediya Janar Tukur Gusau ya rattaba wa hannu, hedikwatar ta ce an soke bikin samun ƴancin kan ne don bai wa sojojin Najeriya damar mayar da hankali kan yaƙi da suke da ta’addanci da ƴan bindiga, kana da bai wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu sararin halartar wani taro mai muhimmanci kan kyautata dangantakar kasa da kasa.

Rundunar ta kuma yi ƙarin haske kan binciken da ake ci gaba da yi kan zargin wasu jami’anta 16 da nuna rashin ɗa’a wajen aiki, inda ta tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa zargin ya dogara ne kan aiyukan soji na yau da kullum, kuma nan ba da daɗewa ba za a bayyana sakamakon binciken ga jama’a.

Shalkwatar Sojin ta yi kira ga ‘yan ƙasa da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro goyon baya da yin biyayya ga Kundin Tsarin Mulkin ƙasar da ma Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Tinubu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: